Wannan dambarwar siyasar duka bita da kulli ne da ake yiwa Rabiu Musa Kwankwaso

0 203

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dukkanin wani kalubale da dambarwar siyasa da yake fuskanta a halin yanzu bita da kulli ne kawai ake yiwa Ubangidansa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Abba Kabir Yusuf ya yi wannan jawabi ne a karon farko tun bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun da ta soke nasararsa yayin taron masu ruwa da tsaki na tafiyar gidan Kwankwasiyya a Kano.

Abba Kabir, yayin da ya bukaci shugabannin jam’iyyar da kada su karaya, ya bukace su da kada su yi musayar kalamai masu zafi da kowa, sai dai su yi amfani da karfinsu wajen zaburar da al’ummar jihar Kano.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da gudanar da dukkan ayyukan da yafara wadanda suka shafi jama’a, wanda suka hada da taimaka wa mata da yara da kuma biyan kudaden fansho.

Leave a Reply

%d bloggers like this: