Gwamna Namadi ya jaddada manufofin gwamnatinsa na ba da fifiko ga fannin ilimin addinin musulunci

0 312

Gwamna Mallam Umar Namad ya bayyana ilimi a matsayin kashin bayan samuwar kowace al’umma da ci gabanta, wanda shi ne babban dalilin da ya sa gwamnatinsa ta kafa hukumar tsangaya domin kula da makarantun Alkur’ani a fadin jihar.

Gwamnan ya halarci bikin rufewa da bayar da kyaututtuka na gasar karatun Alkur’ani na jiha, wanda aka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha ta jiha dake Dutse.

Gasar ta shekara, wadda aka shafe kwanaki ana gudanar da ita a fannin karatun Alqu’ani ta shafi bangaren maza da mata.

Da yake jawabi, Gwamna Mallam Umar Namadi ya jaddada manufofin gwamnatinsa na ba da fifiko sosai wajen bunkasa ilimin Alkur’ani da addinin musulunci a jihar.

Ya ce ilimi shi ne kashin bayan samuwar kowace al’umma da ci gabanta, wanda shi ne babban dalilin da ya sa gwamnatinsa ta kafa hukumar tsangaya domin kula da makarantun Alkur’ani a fadin jihar.

Ya kuma bukaci wadanda suka yi nasara da wadanda suka sha kaye a gasar da su yi farin ciki da kasancewa cikin wadanda suka haddace littafin Allah.

Gwamnan ya yi kira ga wadanda suka yi nasara da su fara shirin tunkarar gasar kasa da kasa. Wadanda suka samu nasarar lashe gasar gaba daya a bangaren maza da mata sun hada da Mohammed Abubakar daga karamar hukumar Babura da Maryam Salihu daga karamar hukumar Dutse.

Leave a Reply

%d bloggers like this: