Wasu ba a san ko su waye ba sun bullo da damfara ta hanyar amfani da lambar waya 081-08763824

0 252

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta yi kira ga al’umma da su yi hattara da ayyukan damfara da wasu da ba a san ko su wanene ba suke yi ta hanyar amfani da lambar waya 081-08763824.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ta ce dan damfara na amfani da hanyoyi daban-daban wajen yada jita-jita mara tushe game da daukar aikin Dan sanda.

Ya ce rundunar ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wani bayani da mutumin ya bayar, domin yaudara ce. Ya yi bayanin cewa domin karin bayani za a iya tuntubar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam a kan lamabar waya 081-31992027.

Leave a Reply

%d bloggers like this: