Gwamnatin jihar Jigawa ta ware N2Bn a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 domin gudanar da wasu manyan aikin tituna

0 259

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware kudi naira biliyan biyu a cikin kasafin kudi na shekarar 2024 domin gudanae da wasu manyan aikin titunan jihar.

Gwamna Malam Umar Namadi shine ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar.

Ya ce an sake gabatar da wasu kudi Naira biliyan biyu a cikin kasafin kudin domin aikin inganta titin Hadejia zuwa Garun Gabas da kuma sanya masa kwalta.

Malam Umar Namadi ya kuma ce an ware naira biliyan biyu da milyan dari biyar domin aikin titin Kwanar Girimbo zuwa Gantsa da kuma Sara.

Ya ce an kuma bada kudi naira biliyan biyar domin gina titunan cikin gari, wadanda suka hada da kammala aikin Wurno da Kanya Babba da fara gudanar da aikin Gumel Bye Pass da Kafin Hausa da Dansure da Gandun Sarki da Bulangu da Aujara da Basirka, da Dangyatum da kuma Sankara. Hakazalika gwamann yace an ware kudi naira biliyan dari bakwai a kasafin kudin domin gina gada da manyan kwalbatoci a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: