Wasu bama-bamai a Kyiv babban birnin kasar Ukraine na cigaba da tashi

0 63

Yanzu haka dai ana samun rahotanni tashin wasu bama-bamai a Kyiv babban birnin kasar Ukraine.

‘Yan jarida a birnin sun ba da rahoton jin karar fashewar wasu manyan bama-bamai biyu a tsakiyar Kyiv da kuma wata karar fashewa mai karfi ta uku a safiyar yau.

Wani tsohon mataimakin ministan cikin gida ya ce ya ji karar fashewar wasu abubuwa guda biyu, inda ya kara da cewa an yi amfani da jirgi ko makamai masu linzami.

Ya zuwa yanzu dai rundunar sojin Ukraine ba ta ce uffan ba.

A halin da ake ciki, shugaban kasar ta Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya tabbatar da harin makami mai linzami da aka kai yau da asuba.

Ya kara da cewa hare-haren na Rasha ya shafi wuraren soji da na fararen hula. A baya dai Rasha ta ce ba ta kai hare-hare kan fararen hula.

A wani labarin kuma, kungiyar Tarayyar Afirka AU ta nuna damuwa kan harin da Rasha ke kaiwa Ukraine tare da yin kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban kungiyar ta AU kuma shugaban kasar Senegal Macky Sall, da shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat.

Leave a Reply

%d bloggers like this: