Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a bankuna hudu da hedikwatar ‘yan sanda a jihar Edo

0 62

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a bankuna hudu da hedikwatar ‘yan sanda a jiya yayin da suka yi wa garin Uromi kawanya a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun isa garin da yawansu kuma a cikin motoci masu yawa kafin su kai hari bankunan hudu da bama-bamai.

‘Yan bindigar da fuskokinsu ke bude, sun kashe mutane biyar da jami’an ‘yan sanda biyu a harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo Bello Kontongs ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce ba shi da wani karin bayani kan harin.

Bello Kontongs ya ce daya daga cikin bankuna hudu da aka kai wa harin na zamani ne.

Ya kuma tabbatar da kashe jami’an ‘yan sanda biyu da fararen hula biyar a harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: