Babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin rufe asusun kananan hukumomin jihar Katsina har zuwa ranar 21 ga Maris, 2022.

Rufe asusun ya biyo bayan kin amincewar da gwamnatin jihar ta yi na biyan tsofin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar ‘yan jam’iyyar PDP da aka sauke ba bisa ka’ida ba tun shekarar 2015.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Salisu Yusuf Majigiri, ne ya bayyana hakan a yau yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar dake birnin Katsina.

Salisu Majigiri ya kuma ce tun da farko kotun koli ta mayar da martani ta hanyar soke matakin da gwamnatin jihar ta dauka a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasarnan.

Kotun ta ce tun a shekarar da ta gabata ta bayar da umarnin cewa, kafin ranar 31 ga watan Agustan 2021, a biya dukkanin hakkokin tsofin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar ‘yan jam’iyyar PDP da aka sauke.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: