Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya koka kan yadda ake samun tabarbarewar harkokin ilimi a makarantu

0 106

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya koka kan yadda ake samun tabarbarewar harkokin ilimi a makarantun kasarnan tare da yin kira da a sake yin garambawul domin tabbatar da ingancin ilimin daliban da ake yayewa daga makarantu.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na kasa na Kungiyar Tsofin Daliban Kwalejin Birninkudu (BIKOBA), Mahmud Ibrahim Kwari, Sule Lamido ya ce rashin ingancin ilimin daliban da suka kammala karatu a makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu ya sa akwai bukatar sake bibiyar manhajar tsarin ilimin kasarnan.

Ya yi nuni da cewa, manyan kalubalen da al’ummar kasarnan ke fuskanta na bukatar kwararru da sauran wadanda suka kammala karatu masu kishin kasa wadanda aka horar da su a makarantun kasarnan a kowane mataki.

Tsohon ministan harkokin wajen kasarnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin majalisar zartarwa ta kungiyar Tsofin Daliban Kwalejin Birninkudu (BIKOBA) karkashin jagorancin shugabanta, Ja’afar Usman Muhammad, a ofishinsa dake Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: