Darakta-Janar na NITDA ya bayar da tabbacin hukumar na hadin gwiwa da Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Jihar Jigawa

0 85

Darakta-Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa, ya bayar da tabbacin hukumar na hadin gwiwa da Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Jihar Jigawa (Manpower) domin bayar da horo kan ilimin na’ura mai kwakwalwa a jiharnan.

Darakta Janar din ya ce hakan ya yi daidai da aikin NITDA na inganta cigaban rayuwar dan Adam ta hanyar aiwatar da tsare-tsarenta.

Kashifu Inuwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Hukumar Gudanarwa na Cibiyar ta Manpower, Inuwa Tahir, da tawagarsa a wata ziyarar ban girma da suka kai a hedikwatar NITDA da ke Abuja.

Darakta Janar din ya ce matakin na hadin gwiwa tsakanin hukumomin biyu ya zo a kan lokaci, ganin yadda bunkasa ma’aikata da inganta ayyukan su ne manyan abubuwan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanya a gaba, wanda ya sa aka kafa wani kwamiti kan yadda kasarnan za ta fita daga cikin koma bayan tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: