Gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyi a manyan makarantu 46 a Najeriya – Ministan Ayyuka da Gidaje

0 63

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyi a manyan makarantu 46 a fadin kasar nan.

Fashola ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da yake kaddamar da hanyoyin da aka gyara tare da sake gina su a kwalejin kimiyya da fasaha ta Hussaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure a jihar Jigawa.

Ministan wanda ya samu wakilcin konturolan ma’aikatar aiyuka ta tarayya a jihar Jigawa, Atewolara Oladele, ya ce 29 daga cikin hanyoyin an kammala su ne a shekarar 2021, yayin da ake shirin mika wasu 17 ga makarantun.

Ya ce ma’aikatar tana gyaran tituna 30 a manyan makarantun kasar nan.

A cewarsa, kimanin mutane 200 aka dauka aiki yayin gyaran hanyoyin a kwalejin ta Hussaini Adamu.

A nasa jawabin, shugaban kwalejin ta Hussaini Adamu, Dakta Sabo Wada, ya ce titunan sun dade da lalacewa kafin gwamnatin tarayya ta kawo dauki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: