Wasu bata gari sun tare wa masu zuwa sallar Tahajju hanya a garin Minna

0 197

Wasu bata gari sun tushe hanyar zuwa Kuta a garin Minna na jihar Neja jiya Juma’a, inda suka kai wa masu zuwa sallar Tahajju hari.

Mazauna yankin sun bayyanawa majiyarmu cewa lamarin ya afku ne da karfe 1 na dare lokacin da masu fita sallar suka nufi masallaci domin gudanar da sallar tahajjudi.

Daya daga cikin mazauna yankin, mai suna Aliyu Isah, ya ce bata garin dauke da muggan makamai sun addabi al’ummar Birnin Minna cikin kwanaki biyar da suka gabata. Kakakin rundunar, ‘yan sandan jihar Neja SP Wasi’u Abiodun, yace jami’an ‘Yansanda nab akin kokarin su wajen fatattakar bata garin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: