‘Yan sanda sun tarwatsa mabiya darikar shi’a a Kaduna

0 103

Akalla mutane hudu ne suka rasu yayin da ‘yan sanda suka yi harbi domin tarwatsa yunkurin mambobin kungiyar yan uwa musulmi ko kuma mabiya darikar shi’a jiya a Kaduna.

An ruwaito cewar mabiya shi’ar sun fito da dama a jihar lokacin da jami’an tsaron suka yin yunkurin dakatar da su.

Sawaba Radio ta ruwaito cewar mabiya shi’ar sun taru a kusa da shatale-tale dake kan titin Ahmadu Bello tun kafin zuwan ‘yan sandan.

Akalla mutane 20 ne suka samu rauni. Sai dai jami’in hulda da jama’in na rundunar yan sanda na JIhar ASP MAnsir Hasan yace jami’an su 3 sun samu rauni yayin da aka dauke su zuwa asibiti domin a duba su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: