Wasu Gwamnoni sun yi kira ga INEC data kaucewa matsaloli a zaben gwamnan da za’a yi a watan Nuwamba

0 258

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP a jiya, sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa data dauki matakin kaucewa matsaloli a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake nuna shakku kan abubuwan da ka iya faruwa a zaben saboda karuwar rashin tsaro a wasu jihohin kasar nan.

A cikin sanarwar da suka fitar a karshen taron kaddamar da kungiyar gwamnonin PDP, karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, gwamnonin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na samar da tsaro mafi aminci ga ‘yan Najeriya.

Ya ce sun lura da tabarbarewar tsaro a kasar nan, musamman kashe rayuka da dukiyoyin jama’a a jihohin Filato da Zamfara da da sauran wasu yankunan kasar nan.

Sun shawarci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su tashi tsaye domin shawo kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: