Gwamnoni su zauna cikin shirin ko ta kwana kan iyuwar samun ambaliya – NEMA

0 365

Darakta Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, ya shawarci gwamnonin kasar nan da su kafa cibiyoyin bayar da agajin gaggawa na cikin gida domin bayar da agajin gaggawa a jihohin su domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa.

Da yake magana da manema labarai jiya a Abuja bayan wani taro da kungiyar gwamnonin Najeriya, daraktan ya dage kan cewa ibtila’in na cikin gida ne saboda haka dole ne a magance su tun daga matakin cikin gida.

Ya ce idan gwamnonin jihohi za su hada kai tare da hukumar NEMA wajen yaki da ibtila’in ambaliyar ruwan, asarar da aka yi a shekarar da ta gabata zata ragu. Ya yi kira ga gwamnonin jihohin da su wayar da kan jama’a kan bukatar yin kaura daga wuraren da ke da hadari zuwa tudun muntsira domin hana asarar rayuka da dukiyoyi da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: