Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun sake kai farmaki jihar Sakkwato

0 64

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kai farmaki kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane uku.

Harin dai ya faru ne sa’o’i kadan bayan gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya bar yankin.

Tambuwal ya ziyarci Sabon Birni ne domin kai ziyarar jaje ga iyalan matafiya da ‘yan bindiga suka kone kurmus a hanyar Sabon birni zuwa Isa ranar Litinin.

Gwamnan ya sanar da bayar da gudunmuwar kudi naira dubu 250 ga iyalan kowane mamaci.

An rawaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 8 na daren jiya, inda suka rika harbe-harbe.

An kasa samun kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, domin jin ta bakinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: