Shugaba Buhari ya bayyana tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande a matsayin cikakken ma’aikacin gwamnati mai nagarta

0 95

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande a matsayin cikakken ma’aikacin gwamnati kamar yadda ake bukata.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da littafin rayuwar Akande da aka yi jiya a Legas.

Buhari ya ce Bisi Akande da rike mutuncinsa a ciki da wajen gwamnati, bai taba karba ko bayar da cin hanci ba.

Shugaban kasa, wanda ya jinjinawa tsohon gwamnan na jihar Osun, ya kuma bayyana Akande a matsayin mutum nagari, mai gaskiya kuma mai son jama’a sannan kuma mai gudanar da mulki matakin farko, wanda halayensa na shugabancinsa ya sa ya zama shugaban jam’iyyar APC na farko.

Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana haduwar sa ta farko da Akande, da kishinsa ga Najeriya, nasarori da rashin jin dadinsa a matsayinsa na gwamnan Osun da kuma irin gwagwarmayar da ya yi na kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: