Ya kamata likitoci masu gwaje-gwaje su kasance masu rike sirrin wadanda suka yiwa gwajin jinya

0 153

Ministan lafiya na kasa Dr. Muhammad Ali Pate, ya bukaci likitoci masu gwaje-gwaje da kasance masu rike sirrin wadanda suka yiwa gwajin jinyar dake damunsu.

Pate yayi wannan kira ne lokacin taron kungiyar likitoci masu aikin gwaje-gwaje a Abuja.

Ministan, ya samu wakilcin daraktan ma’aikatar lafiya ta kasa Dr. Jimoh Salaudeen. Pate, yace ma’aikatar na kokarin ganin an samu cigaba a fannin kiwon lafiya a kasar nan ta hanyar hadin gwiwa da dukkanin wasu kungiyoyin lafiya na duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: