Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karin marasa aikin yi, adadin da ya karu da sama da kaso 33 cikin 100.

Wannan shi ne kaso mafi munin da aka taba gani na marasa aikin yi kasar cikin shekaru 13.

Cikin rahoton da ta fitar, hukumar kididdigar Najeriya ta kara da cewar baya ga matsalar ta rashin aikin yi, a farkon shekarar bara, hauhawar farashi da tsadar rayuwa a kasar ya karu da kaso 16.47 a watan Janairu, yayin da ya karu zuwa kaso 17.33 a watan Fabrairu.

Daga Abuja, wakilinmu Muhammad Kabiru Yusuf ya aiko mana da rahoto.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: