Yan bindiga sun sake kashe mutum 13 da kuma wargaza kauyuka 3 a jihar Zamfara

0 68

Akalla mutane 13 ne aka kashe yayin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu a hare-haren da suka kai tsakanin daren Litinin zuwa safiyar yau a wasu kauyuka 3 dake jihar katsina.

Kauyukan uku wanda suka hada da Guda da Gidan kanawa da Dukawa sun kasance a kananan hukumomin Bakori da Funtua dake kudancin jihar wanda kuma suka yi iyaka da Jihar Kaduna.

Jihar Katsina ta fuskanci hare-haren ‘yan bindiga tun farkon wannan shekarar.

Hari na bayannan sun hada da kisan dagacin wani kauye tare da mutane 4 a kauyen ‘Yan gayya da kuma akalla mutane 12 a kauyukan Ilela.

Mai Magana da yawun ‘yan sanda na Jihar, Gambo Isa ya alakanta harin baya-bayannan da tserewar wasu ‘yan ta’adda daga makwabtan Jihohin Zamfara da Sokoto.

Da yake magana da manema labarai, wani mazaunin garin mai suna Nafi’u Muhammadu yace an kama dagacin garin Guga, Alhaji Umar Guga yayin da aka kashe mutane 10 a harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: