‘Yan bindiga sun yi garkuwa da alkalin kotu a jihar Kaduna

0 164

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata alkalin kotun al’adun gargajiya da ke yankin Sabon Tasha a jihar Kaduna, Janet Galadima tare da ‘ya’yanta hudu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya ce an yi garkuwa da alkalin da ‘ya’yanta hudu a gidansu da ke unguwar Mahuta a karamar hukumar Chikun.

Ya ce daga baya ‘yan bindigar sun kashe babban dan matar mai suna Victor Galadima mai shekaru 14.

A lokaci guda kuma, jami’an ‘yan sanda na sashen Sabon Tasha ne suka gano gawarsa a Ungwan Bayero da ke kauyen Dutse, a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata. Bugu da kari, wata mai fafutukar kare hakkin bil’adama kuma babbar jami’ar zartarwa ta majalisar, Barista Gloria Ballason, ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe dan matar ne bayan da iyalan suka kasa samun kudin fansar da suka nema.

Leave a Reply

%d bloggers like this: