Wani sabon rikici da ya barke da yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane biyu tare da kone gidaje uku a wani sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu ta nan Jihar Jigawa.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa rashin fahimtar da aka samu tsakanin makiyaya da manoma, yasa makiyayan suka gayyaci ‘yan uwansu daga Jihar Katsina, inda suka fara lalata gonaki a kauyukan Safa da Gaurakai dake yankin.
Rahotanni sun ce manoman sun bijire game da lamarin, inda abun ya rikide zuwa rikici tsakanin makiyayan da manoman. Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shi’isu Adam, ya bayyana cewa an kama wasu ’yan asalin yankin biyar da ake zargin sun gayyaci mutanen don tayar da zaune tsaye, yayin da suka bar shanu 15 na makiyayan amma ‘yansanda sun kamo su.