Yan sandan jihar Gombe sun kama wani da ake zargi da satar shanu 23

0 95

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani da ake zargi da satar shanu 23 a kauyen Golombi da ke karamar hukumar Shongom a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi holan matashin mai suna Adamu Maikudi mai shekaru 23 a kauyen Mai Rana da ke karamar hukumar Billiri bisa aikata wannan aika-aika tare da wasu mutum biyu.

Da yake gabatar da wanda ake zargin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, jihar ASP Mahid Abubakar, ya ce wanda ake zargin ya sayar da shanu 23 mallakin wani mai suna Anchau Maishanu, inda ya kara da cewa wasu mutane biyu da ake zargi suna da hannu a cikin lamarin.

Kazalika rundunar ta gabatar da sauran wadanda ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane wajen hada baki da kuma mallakar makamai. Abubakar ya ce, rundunar ta kama Hassan Danladi mai shekaru 25, da Seth Adamu mai shekara 42, da Eli Bulus, mai shekara 22 bayan samun bayanan sirri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: