Za a dauki mataki kan makeran da suke da hannu wajen samar da muggan makamai ga masu aikata laifuka

0 402

Rundunar yan sandan jihar Kano tace zata dauki mataki kan makeran da suke da hannu wajen samar da muggan makamai ga masu aikata laifuka a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Muhammad Gumel, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan kokarin rundunar wajen dakile ayyukan bata gari dake zaune a yankin karamar hukumar Dala ta jihar.

Gumel, yace dukkanin wukake da sauran makamai da aka yi holan su yayin taron, sun nuna cewa ba wai an kera su ne da nufin amfani ga al’umma ba, an yi su ne domin taimakawa bata gari wajen cutar da jama’a. CP Usman, ya kara da cewa tuni ya tura wasika zuwa ga masu sana’ar kira a fadin jihar domin tattaunawa da su, inda zai wayar musu da kai a kan illolin da kera muggan makaman ke haifar wa ga al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: