Hukumar Civil Defence sun tabbatar da kama wasu barayin mai

0 274

Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Legas sun tabbatar da kama wasu barayin mai a yankin Ajah a jihar.

An kame wadanda ake zargi da satar man lokacin wani aikin sintiri da hukumar ke yi domin dakile ayyukan bata gari a cikin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Abolurin Oluwaseun, shi ne ya tabbatar da kama wadanda ake zargin.

Kwamandan hukumar a jihar Usman Ishaq Alfadarai, ya bada umarnin cigaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin.

Ya kuma ce da Zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abin da suka shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: