Kananan hukumomin Birniwa, kiri kasamma da Guri sun kaddamar da kwamitin siyar da taki

0 381

An kaddamar da kwamitin membobi goma sha daya kan sayar da taki a kananan hukumomin Birniwa, kiri kasamma da Guri.

Da yake kaddamar da kwamitin, shugaban karamar hukumar, Hon Umar Baffa na Birniwa, Hon Isah Adamu Matara na Kirikasamna da Hon Musa Shaaibu Guri na karamar hukumar Guri, sun bayyana cewa, an kaddamar da mambobin kwamitin ne bisa umarnin gwamnan jihar, Mallam Umar Namadi.

Shugabannin sun ce za a siyar da kowane buhun takin NPK akan kudi ₦16,000 kawai sabanin farashin kasuwa a yanzu ₦27,000. Shuwagabannin sun bukaci mambobin kwamitin da su tabbatar sun bi ka’idojin gwamnati.

Sun ce kowace karamar hukumar za ta zama wurin siyar da takin da manoma za su iya samu. Sun kara da cewa, duk wanda aka samu yana sayen takin don karkatar da su za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Shugabannin kananan hukumomin wanda sune matsayin shugabannin kwamatin, sun yi kira ga manoman da su tashi tsaye don siyan takin a wuraren sayar wa mafi kusa da su a farashin tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: