Za A Iya Ayyana Karshen Ebola Nan da Watan Disamba – Gwamnatin Najeriya

0 29

Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na iya ayyana ƙarshen annobar Ebola nan da ranar 7 ga Disamba, 2026, idan ba a sake tabbatar da mai ɗauke da cutar ba, ko wanda ake zargi da kamuwa ita, sannan kuma ƙasar ta cika sharuɗɗan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya ce hakan zai dogara ne kan sakamakon bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar da kuma cikar wa’adin kwanaki 42 ba tare da samun mai cutar ba, da Cibiyar Yaƙi da Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) tare da WHO za su jira.

Sai dai Pate ya jaddada cewa wannan ranar ta wucin gadi ce, kuma za ta iya sauyawa idan aka sake gano wani sabon mai cutar.

Bisa ƙa’idojin WHO, ana iya ayyana cewa annoba ta kawo ƙarshe bayan cikar kwanaki 42 a jere ba tare da samun wani sabon mai cutar ba, tare da cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata domin tabbatar da cewa an daƙile yaɗuwar cutar.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner