Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 25 ga Nuwamba domin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fara kare kansa kan zargin tatsar tattaunawar wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta sanya ranar bayan ta yi watsi da buƙatar El-Rufai na a sallame shi ba tare da ya gabatar da kariyarsa ba, bisa hujjar cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da isassun shaidu da za su sa a buƙaci ya kare kansa ba.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta shigar da tuhume-tuhume guda biyar da aka yi wa kwaskwarima a kan tsohon gwamnan.
Tuhume-tuhumen sun samo asali ne daga wata hira da El-Rufai ya yi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun 2026.
A yayin hirar, El-Rufai, ya yi iƙirarin cewa wani mutum ya kutsa cikin wayar Ribadu, wanda hakan ya ba shi damar jin umarnin da ya ba jami’an tsaro na kama shi.
Lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, SAN, ya nemi kotun ta sallami wanda yake karewa ba tare da ya gabatar da kariya ba, yana mai cewa gwamnati ba ta gabatar da isassun hujjojin da za su wajabta masa kare kansa ba.
Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara, Oluwole Aladedoye, ya shaida wa kotun cewa shaidun baki da takardun da aka gabatar sun isa su ba da damar ci gaba da shari’ar.
A hukuncinta, kotun ta amince da hujjar masu gabatar da ƙara, inda ta umarci El-Rufai ya fara gabatar da kariyarsa a ranar 25 ga Nuwamba.
Sai dai matakin kotun ba yana nufin ta tabbatar da laifin El-Rufai ba ne, illa dai ta yanke cewa akwai isasshen dalilin ci gaba da shari’ar tare da ba shi damar gabatar da kariyarsa.