Tinubu Ya Ba da Umarnin Gudanar da Bincike Kan Kisan Sheikh Masussuka

0 23

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga suka harbe shi tare da wani makusancinsa a ranar Litinin a yankin Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina.

Hakan dai na ƙunshe cikin saƙon ta’aziyyar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, inda ya bayyana alhini tare da jajanta wa iyalan marigayin, gwamnatin Katsina da al’ummar musulmi, da duk waɗanda wannan rashi ya shafa.

Tinubu ya tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano waɗanda ke da hannu a mutuwar malamin domin su girbi abin da suka shuka.

Ya kuma yi wa mamacin addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, ya sanya shi a Aljannatul Firdausi.

Wata sanarwar da rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta fitar ta hannun mai magana da yawunta DSP Abubakar Aliyu ta ce an kashe Sheikh Masussuka ne da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Litinin a kofar gidansa da ke karamar hukumar Dutsen-Ma a jihar Katsina.

Sanarwar ta kara da cewa “wani harin ’yan bindiga ne ya yi ajalin malamin tare da wani abokinsa Adamu Abubakar.”

Sakataren Malamin ya ce Masussuka ya fito daga gida ne da nufin tafiya wurin da ya saba gudanar da karatunsa.

Sanarwar ’yan sanda ta ce jim kadan bayan faruwar lamarin ne aka garzaya da malamin da abokinsa zuwa wani asibiti da ke kusa, inda ma’aikatan asibitin suka tabbatar da rasuwar mutanen biyu.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner