NCDC Ta Ce Za A Iya Dage Zaɓen 2027 Idan Cutar Ebola Ta Bazu

0 29

Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ana iya ɗage babban zaɓen shekarar 2027 idan cutar Ebola ta bazu a ƙasar zuwa matakin da zai wajabta ɗaukar matakin domin kare lafiyar jama’a.

Daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television.

A cewarsa, girman ɓullar cutar da kuma yaɗuwarta zuwa yankuna daban-daban ne za su ƙayyade ko akwai buƙatar yin la’akari da ɗage zaɓen.

Sai dai Idris ya jaddada cewa a halin yanzu babu dalilin tunanin ɗaukar irin wannan mataki, yana mai nuna kyakkyawan fata cewa za a shawo kan cutar ba tare da kawo cikas ga jadawalin zaɓen ba.

“ muna fatan ba za a ɗage zaɓen ba, amma idan cutar Ebola ta bazu sosai, za a iya yin la’akari da hakan. A yanzu babu buƙatar ɗaukar wannan mataki,” in ji shi.

Ana sa ran fara gudanar da babban zaɓen 2027 a watan Janairu, yayin da jam’iyyun siyasa da masu neman tsayawa takara suka fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen.

Kalaman shugaban NCDC na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan illar da ɓullar cutar Ebola za ta iya yi ga taron jama’a da sauran ayyukan da za su iya ƙara haɗarin yaɗuwar cutar idan lamarin ya tsananta.

Ya ce duk wani mataki na ɗage zaɓen zai dogara ne kan bukatun kare lafiyar jama’a, ba muradun siyasa ba.

Da yake magana kan zargin cewa gwamnati na iya amfani da ɓullar cutar domin cimma muradun siyasa, Idris ya ce jami’an lafiya ba su da niyyar mayar da cututtuka masu yaɗuwa makamin siyasa.

“Mu a ɓangaren lafiya ba za mu yi amfani da batutuwan cututtuka a matsayin makamin siyasa ba. Babu gwamnatin da za ta yi amfani da cutar Ebola a matsayin makamin siyasa,” in ji shi.

Daraktan NCDC ya bayyana cewa Najeriya ta daɗe tana sa ido kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), inda cutar ta samo asali, kuma ta yi hasashen yiwuwar cutar ta shigo ƙasar.

A cewarsa, zirga-zirgar jama’a, tafiye-tafiyen jiragen sama na ƙasashen waje da kuma ayyukan da ake gudanarwa a mashigai da tashoshin shiga Najeriya na daga cikin abubuwan da suka sa hukumomin lafiya ke ganin yiwuwar shigo da cutar a matsayin abin damuwa.

Ya ce matakan sa ido kan cutar sun dogara ne da abubuwan da ke faruwa a DRC, duk da cewa ba za a iya kawar da yiwuwar shigowar cutar Najeriya gaba ɗaya ba.

“An fara wannan ɓullar cutar Ebola a DRC watanni kaɗan da suka wuce, kuma muna sa ido kan lamarin. Mun san akwai yiwuwar ta shigo Najeriya saboda zirga-zirgar jama’a, jiragen da ke shigowa ƙasar da kuma mashigai. Duk da haka, cutar ta shigo. Babu gwamnatin da za

Leave A Reply

hitta mer om recensioner