Kano: An Gano Gawar Wani Mutum Mai Shekaru 42 A Cikin Ruwa

0 19

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta gano gawar wani mutum mai suna Sani Uba Kwaru, mai shekaru 42, a cikin wani ruwa da ke yankin Dan Agundi a birnin Kano.

Hukumar ta ce ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Hamisu Muhammad da misalin ƙarfe 1 na rana ranar Litinin, inda ya sanar da ita cewa wani mutum ya faɗa cikin ruwan.

A cikin wata sanarwa, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, PFO Kabiru Isah Jafar, ya ce tawagar masu aikin ceto ta garzaya wurin da lamarin ya faru, inda ta gano Kwaru ba ya cikin hayyacinsa.

Hukumar ta buƙaci mazauna jihar da su yi taka-tsantsan a wuraren da ake da ruwa a buɗe da sauran wuraren da ka iya zama masu haɗari.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner