Za ayi rabon kaya ga manoman da ambaliyar ruwa da annobar corona suka shafa

0 91

Asusun cigaban aikin gona na IFAD ya fara rabon kayan aikin gona ga manoma dubu 1 da 178 a jihar Jigawa.

Za ayi rabon kayan ga manoman da ambaliyar ruwa da annobar corona suka shafa a kananan hukumomi 13 na jihar.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Kafin Hausa, Muhammad Usman, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Muhammad Usman yace jami’in cigaban aikin gona na IFAD a jiharnan, Malam Yahaya Buba, shine ya sanar da adadin manoman, lokacin rabon takin zamani da maganin kwari ga manoma 90 da suka ci gajiyar tallafin a karamar hukumar Kafin Hausa.

Ya bayyana cewa jami’in cigaban aikin gonan ya shawarci wadanda suka amfana da suyi amfani da kayan noman ta hanyar da ta dace domin habaka harkokin noma a garuruwansu.

Jami’in yada labaran ya kara da cewa shugaban karamar hukumar Kafin Hausa, Alhaji Muhammad Saminu, ya yabawa Asusun IFAD da gwamnatin jihar Jigawa bisa tallafi da kwarin gwiwar da suke bawa manoma a karamar hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: