Za mu ɗauki ma’aikata kusan miliyan daya da rabi don gudanar da aikin zaɓe cikin inganci – INEC

0 194

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana cewa za ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi kimanin miliyan 1.4.

Waɗanda suka haɗar da masu yi wa ƙasa hidima da ɗaliban manyan makarantun ƙasar da ke shekarar ƙarshe domin taimaka mata gudanar da aikin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Babban kwamishina a hukumar zaɓen kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri’a na hukumar Festu Okoye ne ya bayyana haka ta cikin shirin gidan Talbijin ɗin Arise TV mai suna Morning Show.

Haka kuma hukumar ta gargaɗin masu sayen ƙuri’un mutane da masu ƙirƙirar lambobin katin zaɓen da su daina aikata hakan.

Domin kuwa a cewarsa akwai bayanan kowanne kati a kan na’urarsu ta tantance masu kaɗa lkuri’a, dan haka sayen kuri’ar ba zai amfanar da su da komai ba.

Sai ma cutar da ainihin masu katunan na hana su yancinsu da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su na jefa kuri’a a ranar zaɓen.

Mista Okoye ya ƙara da cewa ”mun bayyana ƙarara cewa hukumarmu za ta kai na’aurar tantance masu kaɗa kuri’a a rumfunan zaɓe, domin tantance masu zaɓe, kuma bayanan kowa na ƙunshe cikin na’urar, a maimakon jikin katin zaɓen”.

”Dan haka abin da kawai jami’in zaɓe zai yi ranar zaɓe shi ne duba lambobi shidan ƙarshe da ke jikin katin zaɓenka, domin fito da bayananka daga cikin na’urar tantace masu kaɗa kuri’ar”.

”Dan haka masu sayen kuri’ar da masu kirkirar lambobin kati za su cutar da masu katunan ne kawai. Ta hanyar hana su yin zaɓe, amma dan ɗaukar katin wani domin bai wa wani ya yi amfani da shi a ranar zaɓe wannan sam ba abu ne mai yiyuwa ba”

A ranar 25 ga watan Fabairun wannan shekarar ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

-BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: