Za’a fara rajistar jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire UTME

0 135

A yau Litinin 15 ga watan Junairu ne za a fara rajistar jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (UTME) ta shekarar 2024.

Hukumar Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) ta bukaci dalibai kada su biya masu cibiyoyin rajistar jarabawar (CBT Center) ko sisi, saboda a cikin kudin fon dinsu har da na rajista a ‘CBT Centre’.

Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Fabian Benjamin ya sanar da cewa JAMB ce za ta tattara dukkan kudaden sannan daga bisani ta biya CBT Center rabonsu.

Hakazalika za a fara sayar da fom din neman gurbin shiga manyan makarantu kai tsaye (DE) da kuma E-pin ranar Laraba 28 ga Fabrairu. A wani cigaban kuma hakumar ta JAMB ta sanar da cewa masu bukata ta musamman dake da sha’awar rubuta jarrabawar zasu yi regista a kyauta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: