Tinubu ya jaddada alkawarin gwamnatin sa na samar da ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta

0 110

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya jaddada alkawarin gwamnatin sa na samar da ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da Abubakar Momoh, ministan raya yankin Neja Delta.

Wata sanarwa da Osigwe Omo-Ikirodah, mataimaki na musamman ga ministan ya fitar jiya a Abuja, ta ce taron ya ta’allaka ne da samar da cikakken bayanai kan ayyuka da kuma tsare-tsaren da ke gudana a ma’aikatar raya Neja Delta.

Ya ce taron an yi shi ne domin neman goyon bayan shugaban kasa da kuma jajircewarsa wajen ganin an samu ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta. Kazalika, ya ce a yayin taron, Momoh ya bayyana muhimman ayyuka da tsare-tsare da ma’aikatar ta yi don bunkasa yanayin zamantakewa da tattalin arzikin yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: