Zaman tattaunawar diflomasiyya domin dawo da zababben shugaba Bazoum ba zai samu tasgaro ba

0 211

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Abdulssalam Abubakar yace tawagarsa data tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a karshen mako abu ne mai matukar dadi.

Jagoran tawagar ta musamman da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta tura zuwa Nijar, yace zaman tattaunawar diflomasiyya domin dawo da zababben shugaba Muhammad Bazoum ba zai samu tasgaro ba.

Abdulsalam, yayin wannan jawabi ne ga manyan shugabannin kungiyar ECOWAS tare da shugaban kasa Bola Tinubu a jiya Talata kan cigaban da aka samu dangane da zaman tattaunawar da suka yi da shugabannin mulkin sojin makobciyar kasar nan Nijar. Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala zaman tattaunawar a fadar shugaban kasa dake Abuja, Abdulsalam, yace babu wani mutum da zai so yaki inda ya cigaba da cewa tattaunawar diflomasiyya ba zata samu tasgaro ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: