Kungiyar manyan likitoci ta kasa za su tsunduma yajin aiki

0 236

Kungiyar manyan likitoci ta kasa ta baiwa gwamnatin tarayya kwanaki 21 domin biyan bukatun ta ko kuma likitocin su tsunduma yajin aiki.

Wannan dai na kunshe cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Talata a karshen taron majalisar zartarwa na na kungiyar da ya gudana ta bidiyon kai tsaye ranar 7 ga watan Augusta 2023.

Takardar sanarwa na dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Dr. Victor Makanjoula, da kuma sakatare janar Dr. Yemi Raji. Dr. Raji, ya tabbatar da hakan ga manema labarai cewa 28 ga watan Auguta ita ce rana ta karshe da suka baiwa gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: