Zamu Bayar Da Haɗin Kai Ga Duk Masu Burin Kawo Cigaban Jigawa – Gwamnati

0 135

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce a shirye take ta mara baya ga duk wata kungiya da hukumomin bada tallafin ayyukan gona, domin cimma burin gwamnati na bunkasa ayyukan gona a jihar.

Babban sakatare a ma’aikatar ayyukan gona na jiha, Alhaji Gambo Ibrahim Aliyu, shine ya bada wannan tabbaci lokacin kaddamar da bita ta wuni daya kan assasa hanyoyin samar da takin zamani da ingantaccen iri tare da inganta ayyukan malaman gona a wannan shekarar ta 2019.

Ya tabbatar da cewa gwamnati mai ci a yanzu, tana namijin kokari wajen tallafawa manoma domin ganin an samar da kayayyakin abinci da na masarufi a wannan daminar, inda ya ce bitar zata karawa manoma karsashi wajen bunkasa ayyukan gona.

Alhaji Gambo Ibrahim Aliyu, ya yabawa jami’an kula da shirin wayar da kan manoma bisa kokarinsu na fadakar da manoman jihar dabarun noma na zamani tare da jaddada kudirin ma’aikatar na marawa shirye-shiryensu baya.

A jawabinsa shugaban kula da shirin wayar da kan manoma na jiha, Dakta Ado Nasir Gumel, ya ce manufar gabatar da bitar shi ne domin samar da hanyoyi da dabaru wajen samar da takin zamani da ingantaccen iri da kuma horar da malaman gona dabarun noma na zamani domin cimma kudirin shirin na bunkasa noman rani da damina.

Daga cikin wadanda suka gabatar da mukalla a lokacin gudanar da taron sun hadar da Farfesa Mai-Kano Ari, da Malam Abubakar Abdullahi Hadejia da Muftahu Abubakar Sankara, dukkaninsu kwararru ne a fanin aikin gona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: