Zamu ci gaba da samar da ababen more rayuwa tare da rubanya kokarin gwamnatinmu – Fintiri

0 141

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya nanata alkawarinsa  na ci gaba da samar da ababen more rayuwa tare da rubanya kokarin gwamnatin sa na ganin an kammala ayukkan da ya gada kafin karshen wa’adinsa. Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai da sadarwa, George Kushi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, a wani taron manema labarai. Ya bayyana kudirin gwamnati na cika alkawuran da ta dauka yayin yakin neman zabe, inda ya kara da cewa gwamnatin ta samu yabo bisa nasarorin da ta samu a bangaren samar da ababen more rayuwa, ayyukan jin kai, da kuma ci gaban bil’adama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: