Zuwa yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 3,840 a birnin Bahar Rum na kasar Libya

0 297

Dubban mutane ne suka bace yayin da masu aikin ceto ke kokarin isa birnin Derna, birnin da ambaliyar ruwa ta fi kamari.

Mazauna birnin Derna na kasar Libya, sun yi ta neman ‘yan uwansu da suka bace, yayin da masu aikin ceto suka nemi karin buhuna domin kwasar gawarwaki, bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta yi sanadin dubban rayuka tare da ratsa wasu da dama zuwa teku.

Ambaliya ta karya wasu kananan hanyoyi a tekun Mediterrenean sakamakon wata guguwa mai karfin gaske da ta mamaye busasshiyar kogin a daren Lahadi, inda madatsun ruwa suka fashe, lamarin da yakai ga rushewar Gine-gine da dama tare da iyalai masu barci a ciki.

Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Laftanar Tarek al-Kharraz a ranar jiya ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ya zuwa yanzu an sami rahoton mutuwar mutane 3,840 a birnin na Bahar Rum, ciki har da 3,190 wadanda tuni aka binne. A cikin su akwai akalla baki 400, akasari daga kasashen Sudan da Masar.

A halin da ake ciki kuma, Hichem Abu Chkiouat, ministan sufurin jiragen sama a hukumar dake kula da gabashin Libya, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters ya zuwa yanzu sama da mutane 5,300 ne suka mutu, ya kuma ce akwai yiyuwar adadin ya karu sosai kuma mai yiwuwa ma ya rubanya. Wasu alkaluma sunce sama da mutane dubu 20 sun rasu tun ranar lahdi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: