Ƙwararrun sojin Rasha sun isa jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin kasar

0 94

Ƙwararrun sojin Rasha sun isa jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin kasar, a daidai lokacin da Moscow ke ci gaba da ƙarfafa tasirinta a yankin Sahel na yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Ƙwararrun sojojin da suka isa Yamai, babban birnin Nijar a ranar Laraba, an gan su suna sauke kaya daga wani jirgin dakon kaya.

Masu horas da sojojin za kuma su kawo tsarin tsaro na jirgin sama, a cewar kafar yaɗa labaran.

Isar su Nijar ya zo ne bayan wata yarjejeniyar baya-bayan nan da aka ƙulla tsakanin sojojin Nijar da ke mulki da Rasha domin haɓaka ƙawancen tsaro. Nijar ta karkata ga Rasha tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a shekarar da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: