Mummunar yunwar da za’a shiga a Sudan ya zarce yadda aka yi hasashe a baya

0 74

Wata ƙungiyar bayar da agaji ta duniya ta yi gargaɗin cewa munin yunwar da za’a shiga a Sudan ya zarce yadda aka yi hasashe a baya.

Ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ta ce ta duba lafiyar dubban ƙananan yara da mata a sansanin ƴan gudun hijira da ke Arewacin Dafur, kuma ta gano cewa ɗaya cikin uku na jimillar su na fama da tsananin yunwa.

A cikin shekara ɗaya, yaƙi tsakanin sojin Sudan da ƴan tayar da ƙayar baya ya tsananta buƙatar ayyukan jin ƙai a sassan ƙasar, musamman a yankin Dafur. Ƙungiyar ta ce aƙalla ƙaramin yaro ɗaya ke mutuwa cikin kowacce sa’a biyu a sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: