Najeriya ta zama kasa ta farko a duniya da ta kaddamar da wani sabon rigakafin cutar sankarau

0 93

Najeriya ta zama kasa ta farko a duniya da ta kaddamar da wani sabon rigakafin cutar sankarau da hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawara.

A cewar WHO, wannan yana da mahimmanci musamman ga ƙasashe kamar Najeriya.

Alurar riga kafin da sauran ayukkan rigakafi suna samun tallafi ne daga, Gavi wanda ke ba da gudummawar tarin allurar rigakafin sankarau na duniya tare da tallafawa ƙasashe masu karamin karfi da rigakafin cutar sankarau na yau da kullun.

WHO ta bayyana cewa sabon rigakafin yana ba da garkuwa mai ƙarfi daga manyan nau’ikan ƙwayoyin cuta guda biyar. Wannan, kamar yadda yana ba da kariya mafi girma fiye da maganin rigakafin da ake amfani da shi a yawancin Afirka, wanda ke da tasiri kawai akan wani nau’in cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: