Ɗangote Ya Buɗe Kamfanin Tumatirin Gwangwani A Kano

0 203

Kamfanin sarrafa tumatiri na Ɗangote ya kafa gidan rainon Tumatiri da kuɗinsa ya tasamma Naira biliyan 3 da ake kira da Green House Nursery a nan Kano, wanda aka tsara zai dinga samar da tan na tumatiri da zai kai Naira miliyan dari uku 300 zuwa miliyan dari uku da hamtsi.

Manajan darakatan Kamfanin Abdulkarim Lawal Kaita ya bayyana hakan yana mai cewar kamfanin na Green House Nursery yace kafa kamfanin na sarrafa tumatiri na Dangote zai kara yawan iri da manoma za su yi amfani da shi wajen noman zamani da kuma na gargajiya a kasar nan.

Abdulkarim Lawal Kaita ya sheda cewar, kafin gwamnatin tarayya ta samar da yawan tumatirin da mutanen kasar za su amfani da shi a cikin gida da kuma fitar da shi zuwa kasashen waje, akwai bukatar a hana shigo da irin tumatire da kasashen waje mussaman ma idan kamfanin ya kafo.

A cewar sa, sabon binciken da kamfanin ya gudanar wajen samar da ingantaccen tumatire kamfanin zai dakile yunkurin gwamnatin tarayya na hana amfani da dala miliyan dari uku da Hamsi ta hanayar hana shigo da tumatirin da ak sarrafa daga kasashen wajen.

Manajan daraktan ya kara da cewar ‘yan Najeriya fiye da miliyan 2 suke amfani da tan din Timatirin da ake sarrfawa, amma kuma sabon kamfanin zai samar da tam miliyan 8 a duk shekara.

Rahoton Freedom

Leave a Reply

%d bloggers like this: