Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Jigawa, ta yi Alla- wadai da harin fashi da makami da aka kai gidan rediyon Radio Nigeria Horizon FM da ke Dutse.
Harin ya haɗa da lalata na’urar transfoma ta gidan rediyon da sace wasu kayayyaki, inda aka rawaito cewa maharan sun ɗaure wasu ma’aikata da igiya tare da gudanar da aikin barnar na tsawon sama da sa’o’i huɗu.
A cikin wata sanarwa da shugaban NUJ na jihar, Isma’il Ibrahim Dutse, da sakatarenta, Aminu Umar Shuwajo, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta nuna alhini ga ma’aikatan da abin ya shafa, tare da fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
NUJ ta yi kira ga gwamnatin Jigawa da hukumomin tsaro su ɗauki matakan kare gidan rediyon da sauran kafafen yaɗa labarai a jihar.
Ta kuma buƙaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, su kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya janyo asarar dukiyoyi da suka kai miliyoyin nairori, ciki har da lalata transfoma da yanke wayoyin lantarki masu kariya.