Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Kawo Karshen Matsalar Tsaro — Bafarawa

0 8

Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya ce a shirye yake ya jagoranci yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027 idan har gwamnatinsa ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya kafin zaɓen.

Bafarawa, wanda ya bayyana hakan a wata hira da RFI Hausa, ya ce zai goyi bayan Tinubu idan aka samu zaman lafiya da zai ba manoma damar komawa gonakinsu ba tare da fargabar hare-haren ’yan bindiga ba.

Ya ce har yanzu shugaban ƙasar na da damar shawo kan matsalar tsaro a sauran watannin da suka rage kafin zaɓe.

“Daga yanzu har zuwa lokacin zaɓe, zan iya yi wa Tinubu yaƙin neman zaɓe da kaina saboda abu guda: idan ya magance matsalar tsaron da ke damun al’ummarmu, wallahi zan zaɓe shi.”

Tsohon gwamnan ya ce al’ummar Arewa sun fi damuwa da tsaro da hanyoyin samun abin dogaro da kai fiye da kashe kuɗaɗe wajen yaƙin neman zaɓe.

Ya bayyana cewa zai fi kyau a yi amfani da kuɗaɗen wajen magance matsalar ’yan bindiga da illolin da suke haifarwa.

Ya ce abin da jama’a ke buƙata shi ne su iya zuwa gonakinsu, su yi sana’o’insu, su samu abin biyan buƙatunsu na yau da kullum, ko da kuwa wasu jami’an gwamnati na karkatar da kuɗaɗen al’umma.

Bafarawa ya kuma nuna damuwa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa, walau ta boko ko ta addini, yana mai gargaɗin cewa makomar yankin na cikin haɗari matuƙar aka ci gaba da hana matasa damar samun ilimi.

“Duk wanda ya tsere maka ta fuskar ilimi, ya tsere maka a komai. Ta yaya zan goyi bayan wanda ba zai taimaka wa al’ummarmu su samu sauƙin wahalhalunsu ba?” in ji shi.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da kada su yi gaggawar yanke hukuncin cewa Tinubu zai faɗi zaɓe, inda ya bayyana cewa ya kamata a auna shugabancinsa bisa abin da zai iya cimmawa a sauran watannin da suka rage.

Bafarawa ya kuma soki shugabannin siyasar Arewa kan rashin haɗa kai domin samar da hanyar magance matsalar tsaro, inda ya ce rarrabuwar kawuna ta ba da gudunmawa wajen jefa yankin cikin halin da yake ciki.

“Mu ne muka jawo wa kanmu wannan matsala saboda mun ƙi haɗuwa da zuciya ɗaya domin ceto kanmu. Babu yadda za a yi mu samu sauƙi ba tare da haɗin kai ba,” in ji shi.

Game da naɗin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin darakta-janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu, Bafarawa ya ce bai ga laifin tsohon gwamnan Zamfara ba da ya amince da aikin.

Ya bayyana naɗin a matsayin hidimar ƙasa, kuma ya jadadda cewa Yari ɗan Najeriya ne, zaɓaɓɓen sanata kuma mamba na jam’iyyar APC, don haka yana da ’yancin karɓar wannan nauyi.

Sai dai ya jaddada cewa naɗin Yari ba ya nufin tabbatar da nasarar Tinubu ko akasin haka, amma dai ana sa ran cewa Yari zai yi iya ƙoƙarinsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Bafarawa ya ce yana cikin dattawan Arewa da suka goyi bayan naɗin Yari, inda ya bayyana cewa sanatan ya tuntubi manyan shugabannin yankin kafin da kuma bayan samun muƙamin, domin neman shawarwari da addu’o’insu.

A cewarsa, babu wani daga cikin dattawan da Yari ya tuntuɓa da ya hana shi karɓar aikin, sai ma dai duk sun taya shi murna da fatan samun nasara.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner