“Zan Iya Sadaukar da Raina Domin Tinubu” — Uba Sani

0 10

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirinsa na kare ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027, yana mai cewa goyon bayansa ga shugaban ƙasar ya samo asali ne daga ƙudirinsa, duk da rashin gamsuwar wasu ’yan Najeriya kan matsin tattalin arziki.

“Ba na neman afuwa kan goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma zan ci gaba da mara masa baya har zuwa minti na ƙarshe,” in ji gwamnan yayin wata hira da shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV ranar Talata.

Da aka tambaye shi ko a shirye yake ya fuskanci suka ko ya ɗauki alhakin siyasa domin kare shugaban ƙasar, Sani ya ce yana da yakinin cewa nan gaba za a tabbatar da cewa matsayinsa daidai ne.

“Zan iya gaya muku a yau, gobe da jibi cewa nan gaba za a tabbatar da cewa matsayina daidai ne,” in ji shi.

Gwamnan ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya samo asali ne, a wani ɓangare, daga dadaddiyar alaƙar da ke tsakaninsu tun shekarar 1994, lokacin da suka shiga fafutukar dawo da mulkin dimokuraɗiyya.

Ya tuna cewa Tinubu, wanda ke da alaƙa da Ƙungiyar NADECO mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya, ya tallafa wa masu fafutukar kawo ƙarshen mulkin soja duk da haɗarin da hakan ke tattare da shi, wanda ya tilasta wa wasu gudun hijira.

Sani ya ce irin abubuwan da suka fuskanta tare a fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya da raba iko tsakanin matakan gwamnati sun taimaka wajen tsara ra’ayinsa game da shugaban ƙasar.

Ya kuma lissafa wasu ayyuka da naɗe-naɗe da ya ce sun amfani Jihar Kaduna a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ciki har da amincewa da shirye-shiryen kafa jami’o’in tarayya guda huɗu da kuma sake gina hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Jami’o’in da ya ambata su ne Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Aiki da ke Kudancin Kaduna, Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zariya, Jami’ar Tarayya ta Albarkatun Man Fetur da ake shirin kafawa a Rigachikun, da kuma shirin mayar da Kwalejin Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) zuwa jami’ar fasaha ta tarayya.

Ya ce waɗannan ayyuka amfanar da jihar ne, ba wata alfarma da aka yi masa da kansa ba.

“Alfarman da ya yi ba gare ni ba ce, domin bai ba ni komai ba. Jihar ce ta amfana,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi nuni da naɗa ’yan asalin Kaduna a manyan muƙaman gwamnatin tarayya, yana mai cewa hakan shaida ce ta wakilcin jihar a gwamnatin Tinubu.

Da aka tambaye shi ko masu zaɓe a Arewacin Najeriya za su sake zaɓar Tinubu duk da matsin tattalin arziki, Sani ya ce ya kamata jam’iyyun adawa su gabatar da sahihin zaɓin da za su bai wa jama’a, maimakon kawai su nemi a ƙi zaɓar shugaban ƙasar.

“Idan kuka ce kada a zaɓi Asiwaju, dole ne ku kawo wanda zai maye gurbinsa,” in ji shi.

Ya ce talauci a Arewacin Najeriya ya wanzu tun kafin gwamnatin Tinubu, amma ya ƙara ta’azzara da shigewar lokaci. Ya kwatanta matsalolin yankin da ginin da ya lalace sakamakon rashin kulawa, har gyaransa ya zama mai wahala.

“Da mun magance wannan matsala tun kafin Asiwaju ya fara tunanin zama shugaban ƙasa, da ba mu kasance a inda muke yanzu ba,” in ji shi.

Gwamnan ya ƙara da cewa a baya ya buƙaci shugabannin Arewa su yi nazari kan ayyukan da suka yi a baya, su kuma amince cewa sun gaza wajen kyautata rayuwar al’umma, amma bai samu isasshen kulawa daga gare su ba.

“Mutanen Arewa su ne matsalar kansu. Bai kamata mu guje wa gaskiya ba. Ina ganin hanya ɗaya tilo ta taimakawa ita ce mu zauna, mu kalli kanmu a madubi, sannan mu amince cewa mu ne matsalar,” in ji gwamnan.

Kalaman Sani na zuwa ne yayin da ’yan siyasa ke ƙara shirin tunkarar babban zaɓen 2027, inda ake sa ran ayyukan gwamnatin Tinubu, matsin tattalin arziki da matsalar tsaro za su kasance manyan batutuwan muhawarar siyasa.

Dangane da matsalar tsaro a Jihar Kaduna, gwamnan ya amince cewa har yanzu akwai damuwa, musamman kan hare-haren da ake kai wa a yankin Millennium City.

Ya ce ya tattauna da jami’an soji da hukumomin tsaro kan lamarin, kuma ana shirin ƙara yawan jami’an tsaro a yankin.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner