Rundunar ‘yan sandan Ogun ta fara tuhumar wasu mutane biyu, Kadir Owolabi da Jamiu Yisa, bayan an kama su da kokon kan mutane uku a yankin Ijebu na jihar. ‘Yan sanda sun fara kama Owolabi ne a ranar Litinin yayin da yake kan babur a hanyar Ijebu Ode/Ibadan dauke da kokon kan mutane.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ta sanar da hakan a ranar Talata kamar yadda Channels TV ta ruwaito.