Gamayyar kungiyoyin kwadago na kasa sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara shekarun ritaya daga 60 zuwa 65, da kuma yawan shekarun aikin gwamnati daga 35 zuwa 40 ga duk ma’aikatan gwamnati.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC), Comrade Joe Ajaero, da takwaransa na TUC, Comrade Festus Osifo, ne suka bayyana wannan bukatar a lokacin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta bana, da aka gudanar a Eagle Square, Abuja.
A yayin taron, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya wakilta, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na da kwarin gwiwar inganta walwalar ma’aikata a kasar.
Kungiyoyin kwadagon sun kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta janye matakin da suka ce ya saba wa kundin tsarin mulki, na dakatar da zababbiyar gwamnati a Jihar Rivers da aka yi karkashin halin rashin tsaro.
Sun bayyana damuwa kan matakan da gwamnati ke dauka da ke hana ‘yancin fadin albarkacin baki, tare da kira da a bude sararin dimokuradiyya domin ci gaban kasa.