Tinubu Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 20 A Kan Karagar Mulki

0 21

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 da hawa karagar sarautar Sarkin Sokoto.

A sakon taya murnar da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya bayyana Sarkin a matsayin jagoran gargajiya wanda mulkinsa ya taimaka wajen bunkasa zaman lafiya, hakuri da juna tsakanin addinai, hadin kan kasa da ci gaba.

Shugaban ya ce Sarkin ya hau karagar mulki ne shekaru 20 da suka gabata cikin tawali’u, jarumtaka da sanin nauyin da ke kansa, inda ya ci gaba da kare martabar Daular Usmaniyya tare da kara bunkasa ta.

Tinubu ya kuma yaba da hikimar Sarkin Musulmi, natsuwarsa a lokutan tashin hankali da kuma gudunmawarsa wajen hada kan Musulmi da Kiristoci.

Ya bayyana shi a matsayin jagoran addini da ke taka muhimmiyar rawa wajen karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiyan addinai daban-daban.

Haka kuma, shugaban ya yaba da kokarin Sarkin wajen inganta zaman lafiya a Arewacin Najeriya da yankin Sahel, da kuma goyon bayansa ga ilimi, musamman na ‘ya’ya mata, manoma da harkokin kiwon lafiya.

Tinubu ya kuma jinjina wa Sarkin bisa kokarinsa na tallafa wa talakawa da masu karamin karfi, yana mai bayyana mulkinsa a matsayin wanda ya mayar da hankali kan jin dadin al’umma.

Shugaban ya yi masa fatan karin lafiya, tsawon rai da hikima, tare da addu’ar mulkinsa ya ci gaba da samar da zaman lafiya a Sakkwato da hadin kai a Najeriya.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner