Gwamnan Bauchi Ya Yi Alhinin Rasuwar Shugaban Karamar Hukumar Zaki A Hatsarin Mota

0 22

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana alhini kan rasuwar shugaban karamar hukumar Zaki, Malam Mas’ud Umar, wanda ya mutu a wani hatsarin mota a kauyen Konkiyal da ke karamar hukumar Darazo.

Rahotanni sun ce marigayin na kan hanyarsa ta komawa Zaki ne bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) da aka gudanar ranar Lahadi, lokacin da hatsarin ya rutsa da shi.

A sakon ta’aziyyarsa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, Gwamna Mohammed ya bayyana marigayin a matsayin ma’aikacin gwamnati mai kishin al’umma, kuma jagoran siyasa da ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Gwamnan ya ce kafin zaben marigayin a matsayin shugaban karamar hukumar Zaki, ya taba rike mukamin Darakta-Janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA), inda ya taka rawa wajen kula da bala’o’i da taimaka wa al’ummomin da ibtila’i ya shafa.

Ya kara da cewa a lokacin da yake shugaban karamar hukumar Zaki, marigayin ya mayar da hankali kan ci gaban matasa da mata da kuma inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Mohammed ya ce duk da karancin lokacin da marigayin ya yi a kan mukamin, ya nuna jajircewa wajen yi wa al’umma hidima da inganta walwalarsu.

Ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Zaki da jihar Bauchi baki daya.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa da abokan arziki da al’ummar karamar hukumar Zaki hakurin jure wannan rashi.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner